1 Timothy 3

1Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau. 2Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa. 3Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba.

4Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, ‘ya’yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma. 5Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah?

6Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis. 7Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis.

8Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba. 9Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi.

11Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai. 12Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da ‘ya’yansu da gidajensu. 13Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu.

14Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba. 15Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al’amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya.

Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: “Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala’iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al’ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa’an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.

16

Copyright information for HauULB